Kamfanin dillancin labaran Koriyar wato KCNA ya kara da cewa, Mista Kim yace a kara inganta makaman ne domin su gano iya karfin barnar da za su iya yi idan aka habasu.
Shugaban yace sai sun sa makiyansu yin nadamar yadda suke musu kallo hadarin kaji. Da kuma irin yadda ake daukar matakan da aka ga dama ga Korea ta Arewa din.
Ko a ranar Alhamis da ta wuce sai da Koriyar ta harba wasu makaman masu cin gajeren zango zuwa cikin teku Harba makaman gwajin da ake zaton sun yi shine a matsayin martani.
Na wani atisayen da sojojin makwabciyar Korea ta Kudu hade da hadin gwiwar na Amurka, wanda Korea ta Arewa ta kira da shirin kai musu mamaya ne.