Hukumar ta hakikanta cewa, akwai kimanin mutane miliyan daya, galibi daga kasashen larabawa da kasashen nahiyar Afrika da suka yi tafiya mai hadarin gaske zuwa Libya da nufin shiga kasashen turai domin samun ingancin rayuwa.
Sai dai, a zahiri idan suka isa kasashen sai suga ba haka lamarin yake ba. Hukumar ta IOM tace ‘yan ci ranin dake Libya suna fuskantar hadura da dama da suka hada da fasa kwauri da safarar bil’adama, da garkuwa da mutane, da kunci, da tsarewa, da kuma gasa masu akuba. Kakakin hukumar Joel Millman yace shirin hukumar dake ba masu sha’awar damar komawa gida, ya maida dubban ‘yan ci rani daga kasashe dabam dabam gida.
Millman yace “Mun hakikanta cewa jiragen saman da hukumar IOM take tanadawa da kuma ayyukan da take gudanarwa a Libya, suna taimakawa wajen maida mutane gida, kuma suna rage hadarin da ‘yan ci rani dake tsallake tekun baharum suke fuskanta.”
Alkaluma sun nuna cewa kimanin ‘yan ci rani da ‘yan gudun hijira daga kasar Somaliya dubu talatin ne suka fice daga Libya, ta cikin teku zuwa kasar Italiya tun shekara ta dubu da dari biyu da goma sha hudu.
Facebook Forum