Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Isa Rasha Don Ganawa Da Putin


Shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong-un, ya isa yankin gabashin Rasha don ganawar sa ta farko da Vladimir Putin, wanda Kim ya ce shine mataki na farko don kusantar dangantaka da Moscow.

A yada zangonsa na farko a kan iyakar birnin Khasan, Kim ya ce wannan "ba zai zama zuwa Rasha na karshe ba, inda ya kara da cewa shi ne mataki na farko don inganta dangantakar Rasha da Koriya ta Arewa, bisa ga wata sanarwa da hukumomin Rasha suka bayar.
Kim yana kyautata zaton samun tallafin tattalin arziki daga Putin a taron na gobe Alhamis- musamman sassauci daga takunkumi na kasa da kasa da aka kakabawa kasarsa, wanda har yanzu ba a janye ba, bayan rugujewar tattaunawar nukiliya da Amurka.
Wannan ne karo na farko na taron kolin da Kim, wanda har zuwa shekarar da ta wuce bai bar Koriya ta arewa ba, tun lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2011.
A cikin shekarar da ta wuce, Kim ya gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump sau biyu, sau uku da shugaban kasar Korea ta Kudu Jae-in, sannan ya gana sau hudu da shugaban kasar China Xi Jinping, sau daya kuma da shugaban kasar Vietnam Nguyen Phu Trong.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG