Kazalika shima friministan kasar Kenya Raila Odinga cewa yayi al’ummar kasar Kenya na marhabin da murnar jin kisan da aka yiwa Osama Bin Laden.A halin da ake ciki, yayin da Amerkawa ke cike da farin cikin kashe Osama bin Laden da sojin Amurka suka yi, amma mai masaukin Osama Bin Laden, wato Pakistan bata fito fili ta nuna murna ko bakin cikinkisan ba.Wata sanarwar da ta fito daga ma’aikatar harkokin wajen Pakistan na cewa duk da cewa sojin Amurka da suka kashe Osama Bin laden sun yi kutse ne cikin kasarta, amma babu wata rawar da Pakistan ta taka a kisan Osama ben Laden. Amma kafofin yada labarun kasar Pakistan a cike suke da babatun kisan na Osama Bin Laden, kuma ‘yan ta’adda na boye da fili suna ta la’antar kisan, kazalika suma tsoffin jami’an Gwamnatin Pakistan, wadansu ma har sun fara yin kiran da a kori Amurka daga Pakistan suka ce tunda Amurka ta cika burinta na kashe jigon kungiyar al-qaida babu kuma abinda ya rage mata tayi a Pakistan. Tasneem Nooran, tsohon Ministan cikin gidan Pakistan yayi hassashen cewa tunda aka kashe uban kungiyar al-qaida yace shi ya san halinsu sarai yanzu zasu nemi ramuwar gayya ne a kan ita kanta Pakistan.