Sojojin kasar Ethiopia sun mamaye manyan hanyoyi da gine ginen gwamnati da kuma filin saukar jirgin sama a yankin gabashin Somaliya bayan tarzomar da ta barke a baban birnin Jigiga da ta zama sanadin mutuwar akalla mutane ashirin da tara.
A ranar Juma’a fada ya barke, bayan sabanin da aka samu tsakanin kananan hukumomi da gwamnati tsakiya.
Ba’a dai tantance abinda ya haddasa tarzomar ba. Wani babban jami’in soja dake tare da jam’iyyar Peoples Democratic ta yankin Somalia mai suna Khadar Abdi Isma’il, ya fadawa Muryar Amurka cewa sojojin taraiyyar ke da alhakin kashe mutanen.
Ya dora laifin barkewar tarzomar akan abinda ya kira nuna fushi akan kutsawar sojoji dauke da makamai ba bisa ka’ida ba cikin birnin. Isma’ila yace an auna unguwanin wadanda ba ‘yan asalin Somali ba ne, aka yi sace sace a cikin shaguna aka kuma kona gine gine har da akalla coci guda daya.
A baya bayan nan gwamnatin Somalia ta zargi jami’an yankunan kasar da laifin keta ‘yancin BIl’Adama.
Facebook Forum