A yau litinin ne Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, yace za’a iya sukar jami’an gwamnati, kuma ba batutuwan tattalin arzikin kasar ba ne kadai suke damun masu zanga zanga. Shugaban ya kuma yi kira da a janye takunkumin da aka saka na hana amfani da shafukan sada zumunta ta intanet.
A lokacin da zanga zanga ta barke kusan sati biyu da suka wuce, gwamnatin ta saka takunkumi akan shafuffukan aika sakonni na sada zumunta wadanda suka kunshi Instagram da telegram. Jami’ai sun cire takunkumin dake kan Instagram a jiya lahadi amman basu cire wanda ke kan telegram ba.
Hamid Shahriari mataimakin shugaban hukumar shari’a ta Iran, ya bayyana a yau litinin cewa, an kame dukkan shugabannin da suka jagoranci wannan "yamutsi" kuma zasu fuskanci hukunci mai tsanani.
Wannan zanga zangar ita ce ta kin jinin gwamnati mafi girma da akayi a Iran tun shekarar 2009. Masu zanga zangar sun koka da rashin ayyukan yi da tashin kudaden abinc, kuma sunyi kira ga gwamntati da ta sabunta harkokin ta. Wasu 'yan zanga zangar kuma sun fito domin su nuna kaunar gwamnati. A kalla mutane 21 ne suka rasu an kuma kame darruruwa.
Gwamnatin Iran ta zargi gwamnatocin kasashen waje da haddasa zanga zangar musamman Amurka da Saudi Arabia.
Ministan harkokin kasashen waje Mohammad Javad Zarif, ya bayyana cewa mutanen Iran suna da ‘yancin da zasu yi zanga zanga, inda yace mabiyan Amurka a kasashen a gabas ta tsakiya ba su da damar yin hakan. Ya kuma fada a taron karfafa tsaro a Tehran cewa, babu kasar da zata iya samun zaman lafiya ta hanyar tada tarzoma a wadansu kasashen.
Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD ya yi wani zaman tattaunawa ranar Jumma’a akan lamarin.
Facebook Forum