Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban IMF Mai Fama Da Tuhuma Ya Yi Murabus

Tsohon shugaban hukumar IMF Dominique Strauss-Khan
Tsohon shugaban hukumar IMF Dominique Strauss-Khan

Shugaban Hukumar Bayar Da Lamuni Ta Duniya (IMF) Dominique Strauss-Kahn, ya yi murabus daga kan mukaminsa a inda yake a tsare a birnin New York, inda ya ke fuskantar tuhuma kan laifin neman yin lalata karfi da yaji.

Hukumar ta IMF ta gabatar da wasikar yin murabus dinsa ne da safiyar yau Alhamis. A wasikar ta Strauss-Kahn mai dauke da kwanan watan jiya Laraba 18 ga watan Mayu, ya ce ya zame masa dole ya yi murabus don ya kare hukumar.

Ya ce ya na son ya yi amfani da dukkan karfinsa, da lokacinsa wajen kare kansa.

Lauyoyin da ke kare shi na kokarin a sake shi kan beli, a daidai lokacin da alkali ke duba yiwuwar tabbatar da tuhuma a hukumance kan wannan mutumin da a baya aka ayyana a matsayin fitaccen dan takarar shugaban kasar Faransa.

Wani jami’in kotu ya bayyana wa ‘yan jarida cewa alkali zai saurari muhawara kan batun belin a yau Alhamis. A farkon wannan satin wani alkali ya zartas da hukuncin cewa wannan hamshakin attajiri dan shekara 62 da haihuwa, dan asalin kasar Faransa na iya tserewa ta jirgin sama.

A halin da ake ciki kuma, an bayar da rahoton cewa ma’aikaciyar otal din da ake zargin shugaban na IMF da tilasta mata yin lalata da shi ta kare zargin da ta ke masa a jiya Laraba.

XS
SM
MD
LG