Kwamishina Filipo Grandi, ya fara wannan ziyara ne a yau Litinin da yankin Diffa inda ‘yan Najeriya fiye da 200,000 da suka gudo daga yankin Arewa maso Gabasin kasar suka sami mafaka kusan shekaru uku kanan sakamakon rikicin Boko Haram.
A lokacin da yake tattaunawa da hukumomin Nijar Filipo, yace zai yi amfanin da wannan damar don ganewa idanunsa zahirin halin da ake ciki a sansanonin ‘yan gudun hijira ko da kuwa na wuni daya ne, domin yin hakan yana da muhimmanci sosai.
Wannan rangadin dai yazo ne a dai dai lokacin da kasar Nijar ke tunanin ta inda zata fullowa mawuyacin halin da ‘yan gudun hijirar Najeriya da Mali kimanin dubu dari biyu da sittin da takwas ke ciki, a yayin da kungiyoyin jin kai ke fuskantar rashin kudi a cewar Fara Minista Brigi Rafini.
Domin kwantar da hankulan kasashen da suka karbi wadannan ‘yan gudun hijira Filipo Grandi, ya bayyana cewa a karshen wannan rangadi na kwanaki goma zai kasance wani cikakken lauyan da ya lakanci ainashin bukatun mutanen da yake karewa. Kuma ya baiwa hukumomin Nijar tabbacin ci gaban ayyukan hukumar UNHCR a kasar.
Bayan kasar Nijar shugaban hukumar UNHCR zai ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar dake Chadi da Kamaru da Najeriya.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Mumuni Barma.