A lokacin da yake bayyana wannan ta shafin Twitrter, Obama ya lashi takobin tado da batutuwan kare hakkin bil Adama a tattaunawar da zai yi da jami’an gwamnatin kasar mai bin tafarkin kwaminisanci.
Wata sanarwar fadar White House kuma ta ce wannan ziyara mai dimbin tarihi, wadda it ace ta farko da wani shugaban Amurka zai kai kasar Cuba a cikin shekaru kusan casa’in, karin alama ce ta kudurin shugaba Obama na shata sabuwar turbar dangantaka tsakanin Amurka da Cuba, tare da kusanto da al’ummar kasashen biyu ga junansu ta hanyar tafiye-tafiye, kasuwanciu da kuma samar da bayanai.
Sanarwar ta ce Obama zai fara ziyarar kwanaki biyu a Cuba dsaga ranar 21 ga watan Maris kafin ya zarce zuwa Argentina.
Wannan ziyara zuwa kasar Cuba ta nuna cewa shugaba Obama ya kuduri aniyar ci gaba da abinda yake gani a zaman wata babbar nasarar da gwamnatinsa ta samu kafin ya sauka daga kan wannan kujera nan da shekara daya.