Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka ya bayyana kisan gillan Colorado a matsayin fitar hankali


Babban jami'in 'yan danda na Aurora Daniel Oates
Babban jami'in 'yan danda na Aurora Daniel Oates

Kwararru a fannin boma-bamai a jihar Colorado dake tsakiyar Amurka sun ce yau asabar zasu sake kokarin shiga gidan da aka yiwa kawanya da bomabomai

Kwararru a fannin boma-bamai a jihar Colorado dake tsakiyar Amurka sun ce yau asabar zasu sake kokarin shiga gidan da aka yiwa kawanya da bomabomai, bayan sun gaza shiga gidan mutumin da ake zargi da kashe mutane da dama jiya jumma’a.

Mutane goma sha biyu aka kashe yayinda wandansu 70 suka ji raunuka jiya da asuba lokacin da ‘yan sanda suka ce James Holmes ya bude wuta a wani gidan silma dake garin Auroro na birnin Denva. Goma sha daya daga cikin mutanen da suka ji rauni suna cikin wani mawuyacin hali.

Hukumomi sun ce, Holmes ya bude wuta ne lokacin da ake kaddamar da sabon silman Batman da ake kira “The Dark Knight Rises.” An kama dan shekaru 24 da ake kyautata zaton ya aikata kisan jim kadan bayan harbe harben.

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana a cikin jawabinsa na mako - mako da ya yi yau asabar cewa, kisan gillan da aka yi a Colorado “abu ne na fitar hankali” kuma idan akwai wani darasi da za a koya daga wannan bala’in shine tuni cewa, rai abu ne na aras.

Mr. Obama yace abinda yake da muhimmanci shine yadda muke dangantaka da junansu, da kuma nunawa juna kauna. Ya kuma yi kira ga dukan jama’a su dauki lokaci su yi addu’a domin wadanda harin ya shafa da danginsu da abokansu, da kuma dangin wadanda tashe tashen hankalin da ba a yayatawa ya shafa tsakanin al’ummominmu kullayomin.

XS
SM
MD
LG