Shugaba Barack Obama yace kasar Amurka har yanzu tana tare da sauran kasashen dake kawance da ita kut-da-kut, sannan an kebance kasar Rasha kana tattalin arzikinta yana cikin matsala.
Mr. Obama ya fadi haka ne a babban jawabin da shugaban kasa yakewa majalisar tarayya kowace shekara da aka fi sani da State of the Union, a daren jiya Talata, inda yace kasar Amurka na shugabanci ne a tsanake, ba da cika baki ba.
Ya kara da cewa yaji wasu mutane suna cewa farmakin da shugaban Rasha Vladimir Putinya kai akan Ukraine hikima ce da nuna karfin iko.
Amma shugaban yace Amurka zata cigaba da tallafawa Demokradiyyar Ukraine, da kuma tabbatarwa kasashen NATO cewa za’a cigaba da yunkurin ganin cewa manyan kasashe basu tsangwama wa kanana ba.
Dangane da yankin Asiya da Pacific kuma, Mr. Obama yace kasar Amurka na sabunta kawancenta da kasashen yankin, da kuma tabbatarwa sauran kasashe su bi dokokin da aka gindaya wajen warware takkadamar iyakokincikin teku.
Dangane da Ebola, shugaban yace yana alfahari da Sojojin Amurka, Likitoci, da ma’akatain kiwon lafiya da kwararru dake taimakawa wajen ceto rayuka da dakile yaduwar cutar.
SAUTI: Shugaban Amurka Obama Yayi Jawabin Shekara-shekara w Majalisun Kasar - 0" http://bit.ly1ukeYOJ
HOTO: Shugaban Amurka Barack Obama
#Hausa #Amurka