Obama zai amshi marabar da aka masa ne da jawabin da zai yiwa ‘yan kasar da ke cike da murnar zuwansa, inda zai fada musu kashin bayan ziyarar tasa da yadda za ta iya kasancewa anan gama don amfanin ‘yan baya da ke tasowa a Amurka da Cuba.
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta bayyana cewa, wannan ziyarar ta Obama da zata dauki kwanaki 3, da kuma jawabin da zai yi wa ‘yan Cuba ta talbijin, to wata manuniyace game da wata sabuwar makoma tsakanin mayakan na cacar baka.
A watanni 8 da suka wuce ne dai aka fara maganar wannan maido da dangantaka tsakanin kasashen biyu a karkashin mulki Shugaba Obama. Obama na kallon wannan a matsayin abin nuna wa ‘yan baya na kyawawan ayyukan bayan gama wa’adin mulkinsa a shekara mai zuwa in Allah ya kaimu.