Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa wadansu fitattun mutane da suka aikata manyan laifuka afuwa a ranar Talata, ciki har da wani tsohon gwamnan jihar Illinois, dan jam’iyyar Democrat da ya taba neman sayar da kujerar Majalisar Dattawa ta tsohon shugaban Amurka Barack Obama.
Trump, wanda a kwanan nan ya wanke sunayen wadansu sanannun mutane da suka taka doka, yayi wa tsohon gwamnan jihar Illinois, Rod Blagojevich afuwa kan hukuncin daurin shekaru 14 da aka yanke masa bayan ya shafe shekaru takwas a gidan yari.
An saki Blagojevich dan shekaru 62 a ranar Talata, wanda da a watan Mayu na shekarar 2024 zai kammala hukuncinsa.
Trump ya kuma yafe wa Bernie Kerik, tsohon kwamishinan ‘yan sanda a birnin New York wanda aka daure a kurkuku kan tuhume-tuhume takwas da suka hada da kin biyan haraji, da kuma Michael Milken, wanda aka same shi da laifin sayar da hannun jari, da kuma Edward DeBartolo Jr., tsohon shugaban kungiyar kwallon kwandon kwararru ta San Francisco da ake kira 49ers, wanda ya amsa laifin gaza bayyana cewa ya ba gwamnan jihar Louisiana cin hancin na dala 400,000 a shekarar 1998, shekaru 20 da suka gabata.
Facebook Forum