Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Zabi Brett Kavanaugh Alkalin Kotun Koli


Sabon alkalin Brett Kavanaugh da shugaba Trump da iyalin alkalin
Sabon alkalin Brett Kavanaugh da shugaba Trump da iyalin alkalin

A wani mataki da watakil zai kasance mafi tasiri a duk tsawon shugabancinsa, shugaban Amurka Donald Trump, ya zabi Brett Kavanaugh, a zaman wanda zai maye gurbin mai shari'a Anthony Kennedy, a kotun koli na Amurka.

"Babu mutum daya a duk fadin Amurka wanda yafi cancanta wajen rike wannan mukami, inji shugaba Trump gameda mutumin da ya zaban, a jawabi da yayi na gabatar da alkalin, da karfe 9 na dare agogon Washington. Ya kira Kavanaugh a zaman "alkali mai basira wanda ya sadaukarda rayuwarsa wajen bautawa al'uma."

Dan shekaru 53 da haifuwa, Kavanaugh, alkali ne mai ra'ayin mazan jiya a kotun tarayya a cikin shekaru nan 12 da kama aiki a zaman alkali. shi dai Alkali Kavanaugh, ba bako bane gameda siyasa a bangaren ofishin Shugaban kasa, da dambarwar dake tattare da haka.

Wani abu guda da zai kasance shine, tantance shi a gaban majalisar dattijan Amurka, zai janyo zazzafar muhawara, a majalisar da 'yan Republican suke da wakilai 51, yayinda 'yan Democrat suke da wakilai 49.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG