Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada batun amfani da maganin zazzabin cizon sauro wajen jinyar cutar coronavirus a jiya Laraba, duk da cewa babban masanin cututtuka masu yaduwa na kasar ya karyata cewa maganin yana warkar da cutar.
Hukumar Abinci da Magunguna ta kasar, wato FDA, kwanan nan ta janye wata doka da ta saka na bada damar amfani da maganin akan matakin gaggawa na maganin COVID-19. Trump ya ce, ya yi amfani da maganin watanni biyu da suka gabata.
Dr. Anthony Fauci, babban darektan Cibiyar kula da Cututtuka masu yaduwa na kasar, ya fada wa shirin labarai na “Good Morning America” na tashar Talabijin ta ABC a shekaran jiya Talata cewa: "Manyan gwaje-gwajen asibiti da aka gudanar kan ingancin maganin hydroxychloroquine sun nuna cewa maganin ba shi da tasiri akan cutar Coronavirus, "
Facebook Forum