Yace haramtaccen al'amarin nan ne na kwarmata bayanai da hukumar leken asiri tayi ya rutsa da Micheal Flynn, kan tattaunawar da yayi da Jakadan Rasha a Amurka kuma, a cewar Trump, "Manema labarai ba su yi masa adalci ba ko kadan."
Da ya ke jawabi a wani taron manema labarai a Fadar White House tsaye ganga da Firaministan Isira'ila Benjamin Netanyahu, Trump bai bayyana dalilinsa na tilasta ma Flynn ya ajiye aiki ba, bayan kwanaki 24 kawai da fara aikin, duk kuwa da cewa Fadar White House ta ce hakan na da nasaba da kara shakkar halin tsohon janar din da Shugaba Trump ke yi.
Ya ce jami'an da ke ta kwarmata bayanan sirri kan tattaunawar Fynn da Jakadan Rasha Sergey Kislyak su na kokari ne su rama irin mummunan kayen da jam'iyyar Democarat ta sha tare da Hillary Clinton, wato tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka da Trump ya kayar a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba.
Amma mai magana da yawun Trump Sean Spicer ya fadi ranar Talata cewa Flynn ya yi bayanin karya ga Mataimakin Shugaban kasa Mike Pence da wasu jami'an gwamnati, makwanni gabanin rantsar da Trump ran 20 ga watan Janairu inda ya gaya masu cewa bai tattauna da Kislyak kan takunkumin da tsohon Shugaba Obama ya kakaba ma Rasha ba.