Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Yace Amurka Zata Iya Kaca-kaca da Korea Ta Arewa


Shugaba Trump a baban taron Majalisar Dinkin Duniya
Shugaba Trump a baban taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaba Donald Truimp ya bukaci kasashen duniya da su hada kai wajen jawa kasar Korea ta arewa burki akan begen ta na kokarin kera makaman niloya.

A jawabin daya gabatarwa baban taron Majalisar Dinkin Duniya, shugaba Donald Trump na Amurka yace tilas kasashen duniya su hada kai wajen tinkarar kasashen Korea ta arewa da Iran da kuma Vebezuela.

Yace Amirka bata da zabi illa kawai tayi kaca-kaca da Korea ta arewa, idan aka tilasta mata kare kanta da kawayen ta daga harin makami mai linzami daga Korea ta arewa.

Akan kasar Iran kuma shugaban na Amirka yace Amirka na iya yin watsai da yarjejeniyar da aka kula da Iran, idan hukumar makamashin atam ta kasa da kasa bata da karfin nazarin shirin nukiliyar kasar yadda ya kamata.

Da ya juya kan kasar Venezuela shugaba Trump yace gwamnatin shugaba Nicolas Maduro tana fama da matsalar cin hanci da rashawa. Shugaba Maduro kusan ya durkusar da kasar sa.

Tunda farko baban sakataren Majalisar Antonio Gueteres ya bude baban taron Majalisar Dinkin Duniya tare da sauran shugabanin kasashen duniya ciki harda shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria.

A jawabin bude taron daya gabatar Antonio Gueteres yayi kashedin cewa begen kasar Korea ta arewa na kera makaman nukiliya shine baban kalubalan da duniya take fuskanta a yanzu.

Yace yaduwar muggan makamai yana hadasa baban hatsari.

Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya, wanda a watan Janairu ya dare kan wannan mukami ya kuma baiyan baraza da sauran kalubalan da duniya take fama dasu daya bukaci a hada kai domin magance su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG