Shugaba Obama yace sababbin dokokin za su kare ‘yancin jama’a da na tsaron kasa.
A safiyar jiya Talata ne majalisar dattawa ta amince da kudurin dokar da masu amincewa su 67, sannan 32 sun hau kujerar naki. Dama a baya majalisar wakilai ta riga ta amince da wannan kuduri.
A karkashin dokar, kamfanonin wayar Amurka amma banda na Cibiyar tsaron kasa ta leken asiri, zasu karba su kuma ajiye bayanan wayoyin ‘yan Amurka. Dole sai masu binciken gwamnati sun samu izinin daga kotu, kafin su binciki duk wani wanda ake zarga da alaqa da ta yiwu dan ta’adda ne.
Gwamnatin Amurka ta fara tattara Lambobin wayoyin jama’a, amma banda bayanan dake cikin kiraye-kirayen tun bayan 11 ga watan satunbar shekara ta 2001. Wannan lokaci ne aka kai hare-haren ta’addanci birnin New York da nan birnin Washington.