Shugaba Barack Obama na Amirka ya kare manufar Amirka a Iran, yana mai fadin cewa Iran tana fuskantar yiwuwar a aza mata takunkunmi da zai durkusarda ita, kuma yanzu an maida Iran saniyar ware.
Shugaba Obama yayi wannan furucin ne a jiya Talata, wajen wani taron yan jaridar a fadar White House. Mr Obama ya jaddada cewa jami’an leken asirin Amirka dana Isra’ila suna zaton za’a iya magance wan nan rikici da Iran ta hanyoyin diplomasiya. Haka kuma yace shugabanin wasu kasashen duniya ba zasu bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.
A yayinda yake nuni da jita jitan da aka ta yayatawa cewa kila Isira’ila ta kaiwa Iran hari, shugaba Obama yace Isira’ila kasa ce mai yancin cin gashin kanta, kuma tilas ta yanke shawarar yadda zata kare kanta.
Shugaba Obama ya kuma ce, baya sa ran za’a samu nasara nan da nan a komawa ga tattaunawar farko da za’a yi tsakanin Iran da sauran kasashen duniya akan shirin nukiliyarta.
Tunda farko a jiya talata, wakilan kwamitin sulhu na dindindin da kasar Jamus sunyi tayin komawa teburin shawarwari da Iran.
Jami’ar da take kula da harkokin kasashen waje na kungiyar kasashen turai, Catherine Ashton jiya talata tace tayi wannan tayi a wata wasikar data rubutawa wakilin Iran Saeed Jalil.
Isira’il da giggan kasashen yammacin duniya suna zargin Iran da laifin rabewa da guzuma tana saran karsana, domin tana rabewa da cewa tana shiri nukiliyarta ne domin samar da makamashi, amma kokari take yi na kera makaman nukiliya. Iran dai ta sha musunta wannan zargi.