Amurka ta amince da zaman Jamhuriyar Sudan ta Kudu a matsayin kasa a hukumance, ranar da kasar ke bukin ayyana ‘yancinta. Shugaba Barack Obama ya bayyana a cikin wata sanarwar yau Asabar cewa, yana fahariya amincewa da diyaucin kasar. Shugaba Obama yace ina fahariyar cewa Amurka ta amince da Jamhuriyar Sudan ta Kudu a matsayin kasa mai cin gashin kanta yau tara ga watan Yuli shekara ta dubu biyu da goma sha daya. Bayan gwaggwarmaya da al’ummar Sudan ta Kudu suka sha, Amurka tayi na’am da kafa sabuwar kasa. Shugaba Obama ya kuma yi alkawarin kulla abota da al’ummar Sudan ta Kudu yayinda suke gina sabuwar kasarsu, da kuma kokari wajen tabbatar da tsaro da ci gaban kasar da kuma tabbatar da shugabancin kwarai. Mr. Obama ya yi kira ga arewaci da kudancin Sudan su aiwatar da cikakkar yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da aka cimma a shekara ta dubu biyu da biyar da ta kawo karshen yaki tsakanin bangarorin, su kuma tattauna kan yadda za a warware rikicin yankin Abyei mai arzikin man fetir. Shugaba Obama ya kuma yi kira ga bangarorin biyu musamman arewaci, su kawo karshen tashin hankali da kuma yiwa mutane barazana a jihar Kordofan dake kudanci wadda ke karkashin ikon arewa. Kazamin fada tsakanin dakarun arewaci da kuma masu goyon bayan Kudanci ya sa duban mutane kauracewa matsugunansu.