Kasashe da dama suna ci gaba da bayyana amincewarsu da kasancewar Sudan ta Kudu sabuwar kasa a duniya mai cin gashin kanta. Wata jaridar kasar Sudan ta laburta cewa, kawo yanzu, a kalla kasashe goma sha biyar ne suka bayyana amincewa da diyaucin kasar, da suka hada da manyan kasashen duniya kamar Amurka da Birtaniya da Rasha da kuma China. Shugaban Amurka Barack Obama yana daga cikin wadanda suka fara bayyana amincewarsu jiya asabar. A cikin sanarwar da ya bayar, shugaba Obama yace Amurka tayi na’am da kafa sabuwar kasar, zata kuma hada hannu da mutanen Sudan ta Kudu yayinda suke aiki tukuru na gina kasarsu. An kuma sami sakonnin amincewa da kasar daga PM Birtaniya David Cameron, da shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev, da kuma shugabannin kasashen Indiya da Kenya da kuma Faransa. Kasar China ita ma ta bayyana amincewarta da cewa, zata yi kokari wajen yayata zaman lafiya da kyakkyawar dangantaka tsakanin Sudan ta Kudu da kuma tsohuwar kasarta Sudan. China ce kasar da tafi sayen danyen mai daga Sudan tana kuma kokarin ganin rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu bai shafi hakar mai ba.
Kasashe da dama suna ci gaba da bayyana amincewarsu da kasancewar Sudan ta Kudu sabuwar kasa a duniya mai cin gashin kanta.