Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ne Ya Kafa Kungiyar ISIS-Trump


Donald Trump dan karar neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican
Donald Trump dan karar neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican

A siyasar Amurka dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, ya zafafa sukar da yake yiwa manufofin shugaba Obama a Iraqi da Syria, ya kira Mr. Obama "mutuminda ya kafa" kungiyar ISIS.

"Shine ya kafa ISIS. Shine ya kafa ISIS. Shine ya kafata. Shi ya kafa ISIS." Trump ya fadawa wani gangamin da magoya bayansa, lokacin yakin neman zabe da yayi a a daren jiya Laraba a Florida.

Trump yaci gaba da cewa "abokiyar kafa wannan kungiya itace "mayaudariya Hillary Clinton."

A baya Trump ya zargi 'yar takarar ta jam'iyyar Democrat Hilary Clinton, cewa ta goyi bayan manufofin da suka kai ga kafa kungiyar 'yanta'ddan da ake kira ISIS. Amma jiya Laraba, Trump da zurfafa zargin da yake yiwa gwamnatin, yana mai cewa kungiyar ta ISIS "a mataki daban daban kun sani-kungiyar tana karrama shugaba Obama." Da aka yi masa tabaya kan wanan ikirarin a safiyar yau Alhamis a shirin tashar talabijin ta CNBC Trump ya sake jaddada wannan zargi, kuma ya sake danganta matsayarsa na adawa da yakin mamaya da Amurka ta kai kan Iraqi da goyon bayan da Mrs Clinton ta yiwa yunkurin, a lokcin tana majalisar dattijan Amurka. Shugaban Amurka Barack Obama wanda baya majalisar dattijai a lokacin, ya bayyana adawarsa da yakin.

.

XS
SM
MD
LG