Buhari ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa ‘yan Najeriya bayan da ya dawo daga hutu da neman magani a Burtaniya.
“Ina samun sauki sosai, ko da yake, akwai yiwuwar nan da wasu makwanni masu zuwa na sake komawa ganin likitoci.” In ji Buhari.
Ya kuma kara da cewa “ina mai matukar godiya ga dukkan ‘yan Najeriya, Musulmai da Kiristoci, wadanda suka dukufa wajen yi min addu’a domin na samu lafiya.” In ji Buhari.
A cewar Buhari, “wannan wata alama ce wacce duk da halin kuncin da ake fuskanta, ‘yan Najeriya sun nuna goyon bayansu ga gwamnati a kokarin da ta ke yi na kawar da kalubalen dake fuskantar kasarmu.”
Najeriya ta shiga halin kuncin tattalin arzikin a ‘yan shekarun bayannan saboda faduwar farashin man fetur a kasuwa duniya kamar yadda masana ke nunawa.
A lokacin wannan jawabi ga ‘yan Najeriyar, shugaba Buhari wanda ke shirin cika shekaru biyu a kan mulki a watan Mayu mai zuwa ya kara jaddada burinsa na ganin cewa ya cika alkawarin da ya yi wa ‘yan kasar.
“Hanyar kawai da zan iya saka maku ita ce na kara himmatuwa wajen yi maku aiki, na kare abinda ku ke so da kuma rike amana. Ina nuna godiyata gare ku.” Ya ce
Maimakon a yi ta tura wakilai daban-daban zuwa Abuja domin su yi min maraba da dawowa, ina kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi ma kasarmu addu’ar samun hadin kai da ci gaba da samun bunkasa.
“Ina fatan Allah ya albarkanci tarayyar Najeriya.” Buhari a karshen jawabinsa.
Domin jin karin bayani saurari wannan rahoto:
Facebook Forum