Sabon shugaban hukumar zaben kasar jamhuriyar Nijer, Issaka Sounna, ya yi rantsuwar kama aiki da kuma alkawarin yin adalci wajan tafiyar da wannan nauyi da aka dora masa.
Ministan cikin gida na jamhuriyar Nijer, Bazoum Mohammed, ya bayyana cewa bikin a matsayin gagarumin ci gaban shirye shiryen da aka sa gaba domin tsara zabubbuka masu tsabta a shekara ta 2021.
Sai dai an gudanar da taron rantsar da mambobin hukumar ne ba tare da halartar wakilan jam’iyyun hamaiya ba, matakin da kakakin kawancen jam’iyun FDDR Alhaji Doudou Mahammadou, ya alakanta da rashin amincewa da hanyoyin da masu rinjaye suka bi domin zaben mambobin hukumar.
A farkon watan jiya ne wani taron majalisar CNDP da bai sami halartar jam’iyun adawa ba ya zabi mutanen da yake bukata shugaba Mahammadou Issoufou, ya nada a matsayin shugaban hukumar zabe da mataimakinsa, matakin da ya haifar da tada jijiyoyin wuya daga wajan ‘yan jam'iiyar hamaiyya ke ganin an yi son kai, zargin da masu rinjaye suka ce ba gaskiya bane.
Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana Karin bayani.
Facebook Forum