Duk da ita ma PDP dan arewa ta tsakiya ne ta zaba a matsayin shugaba wato Iyorchia Ayu daga jihar Binuwai, amma ta yi wata ‘yar dabarar cewa za ta bar kofar takarar a bude ga wanda ‘yan jam’iyya za su zaba ko da daga wane yanki zai fito.
Yayin da ‘yan siyasar kudu ke da matsayar lalle shugabanci a 2023 ya koma yankin su, bayan shekara 8 a arewa, mahawar ta fi tsanani a tsakanin ‘yan arewa inda wasu ke ganin daidai ne wasu kuwa na cewa a’a.
Ga tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau, tura takarar kudu ne mafi a’ala don hakan ne zai taimakawa zaman tare na Najeriya.
A na sa ra’ayin tsohon dan siyasar NEPU Alhaji Hussaini Gariko na cewa babban kuskure ne ‘yan arewa su bari mulki ya kubuce mu su ko da kuwa ba su ji dadin mulkin Buhari ba.
Duk wannan ba shi ne abun da mai sharhi kan lamuran siyasa Bashir Baba ke hangowa ba; don a tunanin sa ‘yan arewa su kan kidime in sun hau kujera.
Da alamun samun matsaya ta uku daga wata tafiyar siyasa da ke shirin zuwa ta wadanda ke ganin APC da PDP ba su yi mu su adalci ba.
Daga Abuja ga rahoton Sale Shehu Ashaka: