Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Na Kokarin Hana Wasu Jiga-Jiganta Komawa APC


PDP da APC.
PDP da APC.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kaddamar da wani yunkuri na hana wasu jiga-jiganta, ciki har da gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle, komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan na Zamfara ya dade yana tuntuba da tattaunawa, akan kudurinsa na sauya sheka zuwa jam’iyyar ta APC, domin cimma burinsa na zarcewa a wa’adin mulki na biyu.

Jam’iyyar APCn ce dai aka ayyana ta lashe zaben gwamnan jihar da ma na ‘yan majalisar tarayya a babban zaben da ya gabata na shekarar 2019, to sai dai daga baya kotu ta karbe ta baiwa jam’iyyar PDP dukkan mukaman da aka yi takara, daga gwamna har ya zuwa ‘yan majalisar dokoki.

To sai dai wasu ‘yansiyasa da ke da kusanci da gwamnan, sun bayyana cewa “Matawalle ya fi ganin alamun yiwuwar samun zarcewa a wa’adin mulki na biyu ne a jam’iyyar APC fiye da PDP a jihar.”

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle

Tuni kuma da gwamnan ya soma tattaunawa a sirrance da jagororin jam’iyyar ta APC a matakin tarayya. Na baya-bayan nan, shi ne ziyarar da wasu gwamnonin APC 3 – Mai Mala Buni na jihar Yobe, wanda kuma shine shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC na kasa, da gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa da kuma gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, suka kai masa a Gusau, babban birnin jihar.

Gwamnonin APC 3 Sun Ziyarci Gwamna Matawalle a Zamfara
Gwamnonin APC 3 Sun Ziyarci Gwamna Matawalle a Zamfara

Duk da yake gwamnonin sun je ne da sunan kaddamar da wasu ayuka bisa gayyatar gwamna Bello Mohammed Matawalle, to amma masu lura da al’amura, da kuma musamman jam’iyyar PDP, sun fassara ziyarar a zaman wata siyasa, kuma wani sashe na kokarin komawar gwamnan a APC.

Karin bayani akan: Aminu Waziri Tambuwal, Bello Mohammed Matawalle, PDP, APC, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Yunkurin farko da PDP ta yi kuwa shi ne aikewa da wata tawagar gwamnoni 6, a karkashin jagorancin shugaban gwamnonin PDP na Najeriya kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Sauran gwamnonin da suka rufa masa baya a ziyarar ta Zamfara, sun hada da Nyesome Wike na jihar Rivers, Bala Mohammed na Bauchi, Darius Ishaku na Taraba, Ahmed Fintiri na Adamawa da Oluwaseyi Makinde na jihar Oyo.

Duk da yake su ma dai sun je ne da suna jajantawa gwamnati da jama’ar jihar akan ibtila’in gobara a babbar kasuwar Gusau, gwamnonin sun yi amfani da damar, inda suka tattauna da gwamnan, suka kuma rarrashe shi da kada ya fice daga jam’iyyar PDP, har ma da ba shi hakuri akan duk wani laifi da aka yi masa.

Gwamnonin PDP Sun Kai ziyara ga Gwamna Matawalle A Zamfara
Gwamnonin PDP Sun Kai ziyara ga Gwamna Matawalle A Zamfara

A yayin da yake maida martani, gwamna Matawalle ya fadawa gwamnonin cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP, haka kuma ya karbi ban hakurin da aka yi masa.

To sai dai binciken da Muryar Amurka ta gudanar, ya bayyana cewa gwamna Bello Mohammed Matawalle yana yunkurin sauya sheka ne ba don an yi masa wani laifi a jam’iyyarsa ta PDP ba, illa dai kawai saboda tabbatar da nasarar burinsa na samun wa’adin mulki na biyu a shekara ta 2023.

Ko bayan wanna ma, akwai rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar ta Zamfara Ahmed Sani Yariman Bakura da wasu gaggan ‘yan APC a jihar, na daga cikin masu son janyo Matawalle zuwa jam’iyyar APC, domin disashe tasirin tsohon gwamna Abdulaziz Yari.

Tsofaffin Gwamnonin Zamfara Ahmed Sani Yarima da Abdulaziz Yari
Tsofaffin Gwamnonin Zamfara Ahmed Sani Yarima da Abdulaziz Yari

An dai tafka siyasar gaske a ziyarorin biyu na APC da PDP a jihar ta Zamfara.

Ko da yake gwamnonin APC sun sirranta batutuwan siyasa a lokacin ziyarar, inda suka maida hankali wajen kaddamar da ayuka da jaje kan bala’in gobara, gwamnonin PDP ko sun fito karara suka caccaki jam’iyyar APC, tare da zargin yin amfani da ziyarar gwamnoninta domin kwace gwamna Matawalle.

“Akwai mamaki yadda APC da gwamnatinta suke kokarin amfani da ibtila’in gobara da jama’ar Zamfara suka shiga domin siyasa, a daidai lokacin da APCn ta kasa tsare rayuka da dukiyoyin jama’a, haka kuma ta kasa sama musu ababen more rayuwa,” in ji Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a lokacin ta su ziyarar.

Wani al’amari ma da ya ja hankalin manazarta lamurran siyasa, shi ne ba da tallafin kudi na naira miliyan 100 ga wadanda balain gobara ya shafa a kasuwar Gusau da Aminu Tambuwal ya ba da sanarwa a madadin gwamnonin PDP a lokacin ziyarar, wanda ya zo kwanaki 3 bayan ziyarar gwamnonin APC, wadanda su kuma suka bayar da tallafin naira miliyan 50 da farko.

Ana sa ran jam’iyyar ta PDP ta aiwatar da yunkurinta na gaba na rarrashin gwamna Matawalle, ta hanyar wata ziyara da shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus zai jagoranci shugabannin kungiyar zuwa Zamfara a yau.

Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP
Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP

Ko bayan gwamnan na Zamfara, PDP na fuskantar barazanar rasa wasu jiga-jiganta kamar gwamnan jihar Cross Rivers, Benedict Ayade, da tsohon Ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode, da Sanata Grace Folashade Bent, wadanda duk aka sami rahotannin cewa suna yunkurin komawa jam’iyyar APC.

Tuni kuma da jam’iyyar ta PDP ta tsara daukar matakan ganin ba ta rasa wadannan jiga-jigan na ta ba, domin kaucewa abinda ya faru a shekara ta 2015, sa’adda Aminu Waziri da sauran wasu jiga-jiganta suka fice zuwa APC.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG