Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar dake Zang-zangar Sako Zakzaky Tayi Watsi da Sakamakon Binciken Gwamnatin Kaduna


Masu fafutikar ganin an sako Zakzaky
Masu fafutikar ganin an sako Zakzaky

Kwana kwanan nan gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sakamakon binciken da tayi akan taho mu gama da 'yan kungiyar shiya da wasu sojojin Najeriya suka yi a garin Zaria, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar 'yan shiyar da dama

Kungiyar Harka Islamiya ta Najeriya dake zanga zamgar ganin an sako Shaikh Ibrahim El-Zakzaky da aka kama biyo bayan hatsaniyar da aka samu tsakaninsojojin Najeriya da mabiya kungiyar shiya tayi watsi da daukacin sakamakon da kuma shawarwari da rahoton kwamitin da gwanatin Kaduna ta kafa.

Malam Abdulrahaman Abubakar Yola shugaban kungiyar masu hankoron an sako Zakzaky ya yiwa manema labarai a garin Kaduna.

Malam Abdulrahaman Abubakar Yola shugaban kungiyar dake hankoron ganin an sako Zakzaky
Malam Abdulrahaman Abubakar Yola shugaban kungiyar dake hankoron ganin an sako Zakzaky

Yace sun fito ne su bayyana matsayinsu akan rahoton binciken da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa. Yace a dunkule rahoton ya nuna Shaikh Ibrahim El-Zakzaky shi yake da alhakin duk abun da ya faru. Yace sun nazarci rahoton sun kuma yi watsi dashi. Yace babu adalci a rahoton.

Yace rahoton ya ba wasu kariya. Mafita ita ce a kafa hukumar bincike ta kasashen duniya mai zaman kanta.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani

XS
SM
MD
LG