Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Ali Abdullah Saleh Yayi Jawabinsa Na Farko


Hoton da aka dauka daga jawabin da shugaba Ali Abdullah Saleh yayi ta bidiyo ga al'ummar Yemen, alhamis 7 Yuli, 2011. Yayi wannan jawabi ne daga inda yake jinya a kasar Saudi Arabiya, makwabciyar Yemen
Hoton da aka dauka daga jawabin da shugaba Ali Abdullah Saleh yayi ta bidiyo ga al'ummar Yemen, alhamis 7 Yuli, 2011. Yayi wannan jawabi ne daga inda yake jinya a kasar Saudi Arabiya, makwabciyar Yemen

A jawabin na bidiyo daga inda yake jinya a Saudi Arabiya, shugaban na Yemen bai nuna alamun zai sauka ba, ko kuma lokacin da zai koma kasar ba.

Shugaba Ali Abdullah Saleh na Yemen ya gabatar da jawabinsa na farko ta hanyar bidiyo ga kasar tun bayan da ya tafi Saudi Arabiya jinyar raunukan da ya samu lokacin wani harin da aka kai na neman hallaka shi a fadarsa a watan da ya shige.

A cikin wannan jawabin da aka dauka ta bidiyo, shugaba Saleh ya ce ya kuna lokacin harin, kuma an yi masa tiyata fiye da sau 8 a Saudi Arabiya mai makwabtaka da Yemen. An ga bandeji a hannunsa a cikin bidiyon na jawabinsa.

A cikin wannan gajeren jawabi nasa, shugaba Saleh bai nuna alamun cewa zai sauka daga kan mulki ba, duk da zanga-zangar da ‘yan adawa suka shafe watanni biyar su na yi kusan kullum da kuma matsin lambar kasashen waje kan ya sauka.

Ya soki lamirin masu adawa da shi yana cewa sun yi ma dimokuradiyya bahaguwar fahimta. Amma yace yana goyon bayan tattaunawa a tsakanin bangarorin siyasar kasar tare da yin marhabin da raba iko wanda bai saba da tsarin mulki ba. Shugaban bai bayyana lokacin da zai koma Yemen ba.

XS
SM
MD
LG