Kasar Isira’ila na fatan yin liyafar rattaba hannu a birnin Washington DC zuwa tsakiyar watan Satumba, saboda yarjajjeniyar da ta cimma da Hadaddiyar Daular Larabawa, Wani babban jami’in gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu ne ya fadi haka yau dinnan Lahadi.
Shugaban Amurka Donald Trump da manyan hadiman Netanyahu, za su tsai da ranar rattaba hannun, lokacin da jami’an na Isira’ila su ka isa Abu Dhabi gobe Litini don tattaunawa, abin da Ministan Harkokin Hadin Kan Yanki, Ofir Akunis ya fada kenan.
Babban Mai Bai Wa Trump Shawara, Jared Kushner da wasu wakilan Amurka za su isa Isira’ila a yau dinnan lahadi don shirya tafiya Hadaddiyar Daular Larabawa din.
Akunis ya kara da cewa gwamnatin Netanyahu na fatan hidimar rattaba hannun, za ta auku gabanin abin da ya kira, “Rosh Hashanah dinmu,” wato sabuwar shekarar Yahudu, wadda ta yi daidai da ranar 18 ga watan Satumba.
Facebook Forum