Kudin da aka gano a Kaduna, kotu taki mayar masa duk da yace abokanansa ne suka bashi kyauta.
Yanzu shirin yana samun nasara saboda 'yansanda sun mayar da kimanin Naira miliyan goma sha takwas da suka samu a gidan Sanata Danjuma Goje kuma tsohon gwamnan jihar Gombe.
Sai dai a Maiduguri cikin jihar Borno EFCC ta gurfanar da mutane biyu gaban kotu wato Buhari Fannami da Bakura Abdullahi domin sun bada labarin da ba gaskiya ba na cewa an binne kudin haram a gidan Bawa Lawal a Pampamari .
Tuni kotu ta tura keyar wadanda ake zargi gidan wakafi.
Gwamnatin tarayya tana karfafawa al'umma gwuiwa da su cigaba da bada bayanin inda aka binne ko boye kudin zarmiya.
Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya gargadi a sanya ido akan hanyoyin fita daga kasar musamman filayen jirgin sama dake Abuja, Legas, Kaduna, Kano da Fatakwal. Wurin cin kudin zarmiya ne yanzu babu shi. Kudaden da aka binne ma a makabarta ana zuwa ana tonosu a baiwa gwamnati.
Inji Garba Shehu 'yan Najeriya sun kwace yaki da cin hanci da rashawa daga hannun gwamnati. Yanzu yakin bashi da iyaka.
'Yan siyasar APC bangaren gwamnati irinsu Inuwa Yahaya na bukatan a cigaba da yaki da cin hanci da rashawa amma da misali domin hana masu kage su dinga kawo labaran da basu da tushe. Yana mai cewa duk wanda ya fito ya bada labarin karya shi ma a hukumtashi.
Bisa tsarin duk wanda ya bada labarin da ya kaiga gano kudi za'a bashi kashi biyar na kudin tare da kare masa suna.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum