Mika rahoton ya zo daidai da lokacin da Shugaba Muhammad Buhari yake shirin komawa Ingila ganin likitocinsa.
Dole yanzu kwamitin ya jira umurnin shugaban kasa ko dawowarsa kafin a bayyana sakamakon binciken da matakan da gwamnati zata dauka. Mukaddashin ba zai bayyana matakin gwamnatin ba domin shi ne ya jagoranci binciken.
Ministan Shari'a Abubakar Malami da mai bada shawara akan harkokin tsaro Janar Babagana Mongunu suna cikin kwamitin binciken.
A cewar Abubakar Malami tunda Farfasa Osinbajo ne ya jagoranci kwamitin ba zai riga malam masallaci ba. Hakkin mataimakin shugaban kasa ne ya yiwa shugaban kasa bayani akan bincikensu. Saboda haka shugaban kasa ne kadai zai iya yin bayani tare da irin matakan da zai dauka.
Kakakin shugaban kasa ya bada tabbacin yin adalci dangane da sakamakon binciken. Yace idan kuma majalisa tayi nata ta kawo shugaban kasa zai duba kuma zai tabbatar an kare abun da ya shafi kasa da bin doka da ka'ida.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum