Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Bude Ofishin Jakadancin Amurka a Birnin Kudus Na Gamuwa Da Tirjiya


Alluma masu nuna hanyar zuwa sabon Ofishin Jakadancin Amurka a Birnin Kudus
Alluma masu nuna hanyar zuwa sabon Ofishin Jakadancin Amurka a Birnin Kudus

Yayin da Amurka ke shirin bude sabon Ofishin Jakadancinta a Birnin Kudus, ana zaman dardar a yankin Gabas Ta Tsakiya saboda shagulgula da kuma zanga-zangar da ka biyo baya.

Yankin Gabas Ta Tsakiya na shirin fuskantar shagulgula da kuma zanga-zanga zuwa ranar Litini a yayin da Amurka ke shirin bude Ofishin Jakadancinta a Birnin Kudus. Kwararru sun ce shawarar da Shugaba Donald Trump ya yanke ta dauke Ofishin Jakadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa Birnin Kudus, tamkar amincewa ce Amurka ta yi da Birnin na Kudus a matsayin babban birnin kasar Isira’ila, al’amarin da ya sha yabo daga Isira’ila ya kuma fusatar da Falasdinawa.

Birnin na Kudus dai ya zake zama fagen labari a daidai lokacin da Amurka ke shirin marabtar baki wajen sama da 800 a wurin bukin bude Ofishin Jakadancinta a kasar ta Isira’ila ranar Litini.

Ivanka, diyar Shugaban Amurka Donald Trump da mijinta Kushner za su kasance a wurin, a yayin da Trump kuma zai yi jawabi ta kafar vidiyo, inda zai jaddada al’amarin a matsayin cika alkawarin da ya yi a watan Disamba na 2017.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG