Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Manoman Najeriya Za Su Ci Gajiyar Gidauniyar Tallafin Da Majalisa Ta Samar Musu?


Wasu manoma a gonarsu
Wasu manoma a gonarsu

A Najeriya, Majalisar Dattawa ta aiwatar da dokar da za ta ba da damar kafa wata gidauniya wadda za ta ba manoma tallafi na taimakon gaggawa.

A Najeriya, Majalisar Dattawa ta aiwatar da dokar da za ta ba da damar kafa wata gidauniya wadda za ta ba manoma tallafi na taimakon gaggawa don kula da noma saboda a samar da abinci wadatacce ga al'umma.

Sai dai wasu na ganin an sake bude wata hanya ne da wasu za su azurta kansu.

Hujjojin kafa wanan gidauniya na nuni da cewa za ta taya manoma wajen magance muhimman matsaloli da ke tattare da noma tare da kammala sauya fasalin nomar daga yadda aka saba yi zuwa noma irin na zamani wanda zai iya samar da ci gaba, da habaka tattalin arzikin kasa da ya tabarbare a ‘yan shekarun baya.

Da yake gabatar da bayanai a kan muhimmancin kafa wanan gidauniya,Shugaban Kwamitin kula da harkokin noma a majalisar dattawa Sanata Abdullahi Adamu ya yi karin haske cewa sashi na 11 na dokar ya tanadi cewa kudade za su hada da tallafin tashi wanda zai zo daga Gwamnatin tarayya,.

Sai kashi 0.5 na Asusun Bunkasa albarkatun kasa, kashi 5 na riba bayan harajin kowane bankin kasuwanci a Najeriya.

Sanata Abdullahi ya kara da cewa akwai kashi 5 na harajin riba na man fetur da kashi 50 na aikin da ake dorawa kan shigo da shinkafa, alkama, sukari, madara, kaji da kifi.

Sauran sun hada da rance na rangwame da lamuni daga kasuwanin hadahadar kasa da kasa.

Shi kuwa, Shugaban Hukumar Habaka Sha'anin Kimiyar noma, Farfesa Abdullahi Mustapha ya yaba da wannan yunkuri inda ya nemi a gaggauta kafa gidauniyar.

Farfesa Abdullahi ya ce ma'aikatarsa za ta shiga cikin gidauniyar domin inganta aikinsu, saboda abu ne da zai ceci kasar daga shiga halin yunwa da ake tsoron zai iya faruwa a sakamakon bullar cutar Korona Bairos da ta hana yin aiyuka na lokaci mai tsawo.

Amma ga kwararre a fanin zamantakewan dan Adam kuma mai nazari a al'amuran yau da kullum Abubakar Umar, ya yi suka ne da kakkausar murya yana cewa ana da bankunan bada lamuni da bashi ga manoma da dama, inda yake ganin ya kamata a hade su a wuri daya domin su yi aiki a karkashin tuta daya.

Mallam Umar yana cewa a wannan yunkuri na kafa gidauniya ta musamman, wata hanye ce kawai za a bude domin wasu su azurta kansu.

Za a aika da dokar Majalisar Wakilai don yin sulhu sannan a mika ta ga shugaban kasa domin ya amince da ita.

XS
SM
MD
LG