Kwamitin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dattawan Najeriya ya zargi Sakataren Gwamnatin da yin watanda da kudin kwangilar yanke ciyawa a arewa maso gabashin Najeriya.
Kwamitin dake karkashin shugabancin Sanata Shehu Sani yace ya bankado wata badakala ta biliyoyin Nera da ta samu hannun Sakataren Gwamnatin Buhari a ciki. Bayan Majalisar ta gudanar da bincike ta sanar da gwamnati ta dauki matakin ladabtar da sakataren. Amma maimakon hakan sai ga wasika daga Fadar Gwamnati zuwa Majalisar inda tayi watsi da sakamakon binciken akan wasu dalilai.
Ga cikakken bayani a shirin Dimokradiya na Sahabo Aliyu Imam.