Kungiyar mai taken KADBAN ta zargi kwamitin majalisar dattawan da rashin zuwa arewa maso gabas domin duba hakikanin aikin da 'yan kwangilar suka yi.
Amma shugaban kwamitin yayi watsi da zargin KADBAN inda yace sun bi daki-daki kuma rahoton da zasu fitar nan gaba zai fayyace yadda aka yi kashe mu raba da kudaden.
Shugaban kungiyar Aji Wala a taron da jagoran kwangilar nome ciyawar Huseni Sunday ya halarta yayi wannan zargi a gaban shugaban kwamitin majalisar dattawa Kwamred Shehu Sani. Yana mai cewa idan sun dauka wani abu ne su cigaba da yi zasu ga abun da zai biyo baya.
Aji Wala ya cigaba da cewa dan kwangilar da yayi aikin yana zaune a wurin taron kuma shi ne PA din Shehu Sani. Baicin hakan dan uwansa Hassan yana majalisar dattawa saboda haka babu abun da ba zai gayawa Shehu Sani ba tunda suna majalisa daya.
Yace akwai abubuwan da suke fadi a boye domin siyasa suke yi. Yace kowa ya san kotun dake tuhumar shugaban majalisar dattawa kotu ce dake karkashin sakataren gwamnatin tarayya.
Shi Husenin da ake magana a kansa yace sun ji dadin aikin da suka yi. Yace ga mutanen kwamiti din kuma sun bayyana gamsuwarsu. Yace amma saboda muradun kansu da manufofinsu sun karyata abun da aka yi.
Amma Shehu Sani yace sun yi bincike sun kuma ga an sace kudin Najeriya na 'yan gudun hijira. Wasu sun azurta kansu kuma kwamitinshi ya gano ko su wanene ne.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.