Bayan karshen yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki biyar da suka cimma domin aiwatar da aikin jinkai, Saudiya da kawayenta sun soma kai hare-hare akan ‘yan tawayen Houthi cikin kasar Yemen.
Jiya Lahadi aka kawo karshen yarjejeniyar kuma wa’adin na cika Saudiya da kawayenta suka shiga kai hare-hare a sansanonin ‘yan Houthi da suke Birnin Aden, Birnin dake da tashar jiragen ruwa.
Tun karshen watan Mayu Saudiya da kawayenta suke ta yin lugudar wuta akan ‘yan tawayen Houthi dake samun goyon bayan kasar Iran. Tun a lokacin ‘yan tawayen suke rike da Birnin Sana’a.
A safiyar jiya Lahadi shugabannin siyasa na kasar Yemen suka yi wani taro a Riyadh fadar gwamnatin Saudiya inda suke tattaunawa da nufin samo bakin zaren warware rikicin. To saidai babu wakilin ‘yan Houthi da ya halarci taron.
Dama can su ‘yan Houthin sun yi watsi da manufar taron nakwana uku da suka hada da maido da shugaban kasar da duniya ta amince dashi Abdrabbu Mansour Hadi kan mukaminsa.
Mr. Hadi ya shaidawa mahalarta taron cewa jama’ar Yemen suna jiran wanzuwar zaman lafiya wanda ba zai yiwu ba sai an mayarda gwamnatin da duniya ta amince da ita kan mulki. Ita ce halal. Abu na biyu shi ne a kwace makaman ‘yan Houthi su daina fada.
Mr. Hadi ya yi watsi da yadda ‘yan tawayen suka kwace gwamnati bara bayan da aka cimma yarjejeniyar yadda za’a raba iko a kasar.
Alkalumma da MDD ta fitar sun nuna cewa kawo yanzu mutane 1,500 suka rasa rayukansu sanadiyar fadan da ake yi. Mutane 6,200 suka jikata kana 450,000 suka rasa muhallansu.