Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sashen Hausa Na Muryar Amurka Ya Gudanar Da Taron Hadin Kai A Abuja


Sashen Hausa na Muryar Amurka ya gudanar da taron tattaunawa ta musamman tsakanin wakilan addinin Muslunci dana Kirista a Abuja.

Taron tattaunawar dai ya samu halartar wakilan mazhabar Shi'a da Izala da kumaTijjaniya, sai kuma rundunar yan sanda da Lauyoyi da jami'an tsaro, masu kare hakkin mata da jami'an gwamnati da kuma Pasto Aminci a bangaren addinin Kirista.

Haka kuma taron ya duba muhimmancin bin dokokin kasa da kaucewa fito-na-fito da jami'an tsaro tare da bin ka'idar fitowa zanga-zanga ga kungiyoyin dake da irin wannan tsari.

Dr. Umar Labdo shine ya wakilci kungiyar Izalatul Bidi'a wa Iqamatus-Sunnah (JIBWIS), ya yin da Muhammad Ibrahim Gamawa ke wakiltar Mazhabar Shi'a, Muhammad Alkasim Yahya a matsayin wakilin Ansaruldin Attijjaniya, inda suka baiyyana jin dadinsu game da taron, da kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Pasto Aminci Abu da tsohon shugaban reshen matasa na kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Pasto Simon A.S Dolly, sun halarci taron a madadin mabiya addinin Kirista.

Irin waddan taruka kan taimaka wajen fahimtar juna da zai iya zama yunkuri kan wanzar da zaman lafiya a kasa.

A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Hauwa Umar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00



Facebook Forum

XS
SM
MD
LG