Sarki Salman na Saudiyya ya karawa dansa Mohammed Bin Salman mai shekaru 31 girma, zuwa mukamin Yarima, wanda hakan ya saka shi a matsayin wanda zai gaje shi, yayin kuma da shi dan nasa ke rike da mukamin ministan tsaron kasar da kuma jan ragamar wani shirin yi wa tattalin arzikin kasar garanbawul.
A yau Laraba aka sanar da wannan sauyi a karkashin wata doka, wacce kamfanin dillancin labarai mallakar kasar na SPA ya sanar.
Gabanin baiwa dan nasa wannan mukami, dokar ta nuna cewa Sarki Salman ya sauke Mohammed Bin Nayef, wanda shi ya kamata ya gaje shi daga mukaminsa, sannan ya kuma sauke shi daga mukamin Ministan cikin gida da yake rike da shi.
Shi dai Sarki Salman kawu ne ga Mohammed Bin Nayef da ya sauke.
Har ila yau dan nasa, Mohammed Bin Salman, wanda a da shi ne mataimakin Yariman kasar, zai kuma rike mukamin mataimakin Firai ministan Saudiyya.
Wannan sauye-sauye, ya biyo bayan amincewa da majalisar iyalan masarautar ta yi, inda 31 daga cikin mambobin majalisar suka amince da sauyin.
Facebook Forum