Olisa Metuh yayi bayanai dake nuna cewa jam’iyyar zata farfado don shirin karbar gwamnati a shekara ta 2019, Metuh dai fitowarsa kenan bayan samin belin zargin badakalar kudi Naira miliyan dubu da miliyan ‘dari hudu.
Yace wutar rikicin da ya afkawar jam’iyyar ta bangaren kama madafin iko tun marabus ‘din Ahmed Mu’azu, ya biyo bayan yanayin PDP ne na mutunta dimokaradiyya, tuni dai tsofin ‘yan jam’iyyar irin su Alhaji Yahaya Abba daga jihar Borno, ke marawa matakan da tsohon mai baiwa shugaba Jonathan shawara ta fuskar siyasa Ahmed Gulak yayi na kai jam’iyyar kotu da ayyana ture Uches Sekundes a matsayin shugaban rikon kwarya.
Alhaji Baffa yace shi ma zai kai PDP kara kotu don mayar masa kudaden cike takardun tsayawa takarar ‘dan majalisar dattawa daga Borno, da yace rashin yin zaben fidda gwani ne yasa aka kawar da shi can gefe ya koma AFGA, tare de tsohon ministan labaru Labaran Maku.
Haka nan masana na cigaba da mahawara kan hukuncin kotun koli da ya soke kujerar ‘yan majalisar PDP guda biyu Andy Ubah da Stella Odua, tun jam’iyyar bata murmure daga wannan hukunci ba, sai babbar kotun tarayya ta soke zaben wani ‘dan majalisar wakilai da majalisar zabe ta tsayar.
Yanzu haka dai tasirin kotu a harkar zabe a Najeriya, kan saka zulumi a zukatan masu rike da kujerun siyasa, ko suna da gaskiya sukanyi fargaba har sai shari’a ta kaya.
Saurari rahotan Madina Dauda daga Abuja.