Shugabar kasar Argentina ta yi alkawarin kara sadaukar da kai ta yiwa kasar ta aiki a lokacin da za ta yi jiyyar cutar sankarar makogwaro, bayan an yi ma ta aikin fida.
A fitar ta, ta farko bainar jama'a jiya a jiya Laraba tun bayan da aka yi sanarwar kamuwar ta da cutar, shugaba Cristina Fernandez de Kirchner ta na cikin kuzari da walwala. Ta ce za ta maida hankali sosai kan mataimakin ta wanda zai tafiyar da harakokin mulkin kasar lokacin da za ta yi hutun jiyya na kwanaki 20, har ma cikin raha, ta yi zolayar cewa ya kamata mataimakin na ta , ya shiga hankalin shi.
Ranar Talatar da ta gabata wani kakakin gwamnatin kasar ya yi sanarwar cewa a makon jiya likitoci sun gano cewa shugabar ta na da sankarar makogwaro. Kakakin ya ce cutar sankarar ba ta nuna alamun bazuwa da gama jiki ba, kuma idan aka yi jiyyar ta, ta na warkewa da kyau. A makon gobe za a yiwa shugabar kasar aikin fida a babban asibitin Austral, a Buenos Aires babban birnin kasar na Argentina.
A shekarar da ta gabata, shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya yi jiyyar cutar sankarar mara a kasar Cuba, shi ma tsohon shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya fara jiyyar cutar sankarar makwallato. Haka ita ma shugabar kasar Brazil mai ci, Dilma Rousseff, ta yi jiyyar cutar sankara jim kadan kafin ta kama aiki a cikin watan janairun da ya gabata.
A cikin wani jawabin da ya yi ta talbijin ja iya Laraba, Mr.Chavez mai fitowa fili karara ya na sukan lamirin Amurka akai-akai, ya ce watakila ma Amurka ce ta ke bin shugabannin kasashen kudancin nahiyar Amurka ta na hada su da cutar sankara cikin wani shirin ta na mugunta da nufaka.