WASHINGTON, DC —
Dan majalisar dattawa mai wakiltar kudancin jihar Borno ya tsallake rijiya da baya sakamakon jefa wasu bama-bamai da jirgin mayakan saman sojojin Najeriya ya yi kan tawagarsa.
Ranar Asabar da ta gabata Sanato Ali Ndume shi da tawagarsa suka fito domin zuwa yin ta'aziya da jajantawa wasu 'yan mazabarsa kan harin da aka kai masu da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane da kuma kone gidajen wasu. Da suka isa wani kauye da ake kira Pulka kan hanyarsu ta zuwa garin Gwoza sai suka ji an soma saka masu bama-bamai ta sama wanda hakan ya tilastasu neman mafaka. To amma babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni sakamakon harin.
Sanato Ali Ndume ya ce yayin da suke tafiya a cikin motoci shida sai suka soma jin fadowar bama-bamai har sau hudu a gabansu. Da farko Sanaton ya dauka cewa 'yan Boko Haram ne suka jefa masu ko kuma sun dana bama-bamai a kan hanyar da suke tafiya. Sojojin da suke yi masu jagoranci suka ce jirgin sojojin mayakan sama na Najeriya suka jefa masu bama-bamai. Sanato Ndume ya ce lamarin ya bashi mamaki. Ya ce an yi sa'a ba'a rasa rayuka ba. Ya godewa Allah babu wanda ya rasu ko ya ji ciwo hatta wadanda suke bakin hanya. Ya ce shi yana gani rashin iya aiki ne.
Sanato ya ce kafin su kama hanya sun shaidawa jam'an tsaro dalili ma ke nan da suka bashi sojoji su yi masa rakiya. Ya yi magana da manyan jam'an tsaro aka bashi sojoji bakwai da 'yansanda biyar. Bayan aukuwar lamarin gwamnan jiharsa ya samu labari kuma shi sanaton ya shaidawa manyan jam'an tsaro abubuwan da suka faru.
A wani lamarin kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar Demboa Peter Guntabiye wanda yana cikin kwamitin harkokin aikin soja kokawa ya yi da irin saken da sojoji ke yi har aka kone gidansa da wani coci kurmus a cikin garin Gwozan. Ya yi furucin ne domin ya shaidawa jami'an tsaro cewa maiyiwuwa za'a kai hari kan garin nasu. Ta bakin shi dan majalisar ya ce sati uku da suka wuce ya fada ma sojoji cewa ya ji wai za'a kawo hari kan garin nasu domin haka su dauki matakan tsaro domin dakile aukuwar yin hakan. Ya ce sau uku yana kiransu basu dauki waya ba sai daga baya wani Lutenan Rabiu ya dauka amma ya ce shi baya shiyar an sake masa wurin aiki.Ya kirasu yayin da ake kone gidansa da mijami'a amma babu abun da suka yi. Ya ce an fara kone gidannsa da masujada tun karfe takwas na safe amma basu ga jami'an tsaro ba sai karfe tara na dare. Ya ce ya kira babban kwamanda wanda ya ce tun makwanni uku da suka gabata ya tura jam'an tsaro wurin lamarin da mutanen kauyen suka musanta.
Ga karin bayani.