Kungiyar matasan arewa ta ‘Northern Youths Assembly’ (NOYA) ta yi kira musamman ga zababben shugaban kasa da ya marawa aniyar Sanata Barau Jibrin baya ta zama shugaban majalisar dattawa, inda ta bayyana cewa matsayinsu ya samo asali ne sakamakon biyayyar Sanatan Kano ga jam’iyya mai mulki ta All Progressives. Congress (APC).
Kamar yadda wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun babban jami’in kungiyar ta NOYA na kasa, Dr Suleiman Mustapha Gombe, kuma aka raba wa manema labarai a Bauchi a ranar Lahadi, tana mai cewa farin jini, karamci da nasarorin da Jibrin ya samu ya ceci APC daga durkushewa gaba daya a jihar Kano.
Kungiyar ta bayyana cewa: “Da ace jam’iyyar APC ta rasa Sanata Barau Jibrin a cikin rigingimun da aka dauki tsawon lokaci ana yi da jam’iyyar a jihar Kano, lokacin da ‘yan majalisar wakilai bakwai daga jihar, karkashin jagorancin mai girma Sanata Ibrahim Shekarau suka kafa gaggarumin bangaren da suka kira G7 don su kalubalanci abin da suka dauka a matsayin babban rashin adalci da shugabancin jam'iyyar APC a jihar Kano ya yi musu, kashi 85% na kuri'un da APC ta samu a jihar Kano a zaben shugaban kasa da ya gabata inda shi (Tinubu) ya yi nasara, toh da dan takarar shugaban kasa na NNPP kadai ne zai kasance mafi farin jini a jihar Kano.
"Shaharar da Barau Jibrin ya nuna, da kyautatawarsa da kyawawan nasarorin da ya samu ne suka ceci jam'iyyar daga rugujewa gaba daya a jihar Kano."
Kungiyar ta gabatar da cewa, domin tabbatar da adalci, daidaito da gaskiya, ya kamata a mayar da matsayin Shugaban Majalisar Dattawa zuwa yankin Arewa maso Yamma, inda Jibrin ya fito, inda ta kara da cewa a tarihin siyasar Najeriya, al’ummar shiyyar Arewa-maso-Yamma bata taba samar da Shugaban Majalisar Dattawa ba tun zuwan dimokuradiyya a kasar nan.