Bayan wani taro da suka yi a birnin Paris da bai samu halarcin wakilan Palsdinawa dana Isira’ila ba, shugaban Faransa Francois Hollande yayi watsi da masu yada jita jita da tababa, wadanda tuni suka ce babu yadda za’a yi a kafa kasar Paleasdinu.
Taron na samun zaman lafiya, wanda shine na biyu da Faransa ta dauki dawainiyar gudanarwa cikin kasa da shekara daya, sanarwa bayan taro tace za’a sake yin wani taron samun zaman lafiya kafin karshen wannan shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai idan Allah ya yarda.
Wasu suna baiyana tsoron cewa Donald Trump, wanda kila ya fi nuna kaunar tsugunar da Yahudawa yan share wuri zauna da Isira’ila ta ke , ya maida ofishin jakadancin Amirka a Isira’ila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Qudus, matakin na iya jawo barazanar ga begen kafa kasashe biyu Isira’ila da Palasdinu masu makwaptan juna a zaman hanyar data fi dacewa na samun dauwamamen zaman lafiya a yankin ko kuma tsakanin bangarorin biyu.