Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama da mutane dari da arba’in sun halaka a jumhuriyar Demokuradiyyar Congo a wani hatsarin kwale-kwale


Rahotanni daga kasar Congo na cewa sama da mutane dari da arba’in ne suka halaka a jumhuriyar Demokuradiyyar Congo, a dalilin afkuwar hatsarin kwale-kwalen dake cike makil da mutane wanda ya kife a ruwa.

Rahotanni daga kasar Congo na cewa sama da mutane dari da arba’in ne suka halaka a jumhuriyar Demokuradiyyar Congo, a dalilin afkuwar hatsarin kwale-kwalen dake cike makil da mutane wanda ya kife a ruwa. Jiya Alhamis aka ji jami’an Gwamnatin Congo na cewa hatsarin karamin jirgin ruwa ya afku ne a tafkin ruwan Congo lardin yammacin Bandundu. Ministan labarai, Lambert Mende yace mutane tamanin ne aka tabbatar da mutuwarsu, amma jami’an karamar hukumar da hatsarin ya faru sun ce yawan wadanda suka halaka nada yawa. An kyuatata cewar akwai fasinja sama da metan a karamin jirgin ruwan, sannan kuma aka laftawa jirgin kaya daga Bandundu zuwa birnin Kinshasa. Jami’an ayyukan ceto na can suna ci gaba da bincike a ruwa domin ganin ko za’a iya samun wadanda suka kubuta.

XS
SM
MD
LG