Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siriya da Saudi Arabiya, da Lebanon, sun yi taron a birnin Beiruit


Sarki Abdullah na Saudiyya,da Bashir Assad na Siriya da,shugabannin Lebanon sun yi taro a birnin Beiruit da nufin kore zaman dar- dar, gabannin a fidda sakamkon bincike kan kisan gilla da aka yi wa PM Lebanon.

Ranar Jumma’a ce Shugabannin kasashen Syria, da Saudiyya, da kuma Lebanon, suka gana birnin Beirut da nufin warware zaman dar dar da ake yi,dangane da yi yu war a tuhumi wasu wakilan Hezbollah, bisa zargin kisan gilla da aka yi wa PM Lebanon, Rafik Hariri.

Shugabn Syria Bashar al-Assad, da sarki Abdullah na Saudiyya, sun yi shawarwari da shugaban Lebanon Michel Suleiman, da PM Sa’ad Hariri, dan PM da aka kashe da wasu jami’an kasar.
Wakilan majalisar dokokin kasar daga bangaren Hezbollah, suma sun halarci shawarwarin da aka yi a fadar shugaban kasar.

A jawabin bayan taro da aka bayar “shugabannin sun jaddada muhimmancin zaman lafiya,da bukatar ‘yan kasar Lebanon su himmatu wajen kaucewa tada tarzoma”.

XS
SM
MD
LG