Al’umar yankin mutum na farko da aka samu da cutar Coronavirus a jihar Filato ta yi barazanar garzayawa zuwa kotu domin a bi mata kadinta.
Jama’ar yankin na kulabalantar yadda suna da bayanan yarinyar da cutar ta COVID-19 ta harba ya karade shafukan sada zumunta duk da cewa sun ba da hadin kai ga hukumomi.
“A matsayinmu na al’uma ba a kyauta mana ba, domin in ka ce kai daga unguwar kake, za ka ga ana gudun mutanenmu” In ji Shugaban matasan yankin, Muhammad Shugaba.
Ya kara da cewa, “kamar yadda muka janyo hankalin gwamnati, idan ba su yi wani abu a kai ba, za mu iya tafiya kotu.”
A cewar shugaban matasan, suna kuma bukatar a sake yin gwajin domin a tabbatar da sahihancin sakamakon.
Sai dai Kwamishinan yada labarai a jihar, Mr. Dan Manjang, wanda ya nemi afuwan jama’ar yankin, ya ce tuni gwamnati ta kaddamar da bincike kan lamarin.
“Wadannan mutane an riga an ba su takardar tambaya (tuhuma) da su ba da nasu bayanin kan abin da suka sani a kai, a yi hakuri.” Manjang ya ce.
Wannan ala’amari na faruwa ne, kwana guda bayan da wasu al’umomin jihar ta Filato, suka yi zanga zangar nuna kuncin da suka shiga na rashin sanadiyyar dokar kulle da hukumomin jihar suka ayyana.
Amma gwamnatin jihar ta yi ikrarin cewa “tunzura” mutanen aka yi sannan tallafin da ta fitar na gidajen marayu ne da marasa galihu.
Ya zuwa yanzu mutum daya ne aka tabbatar ya kamu da wannan cutar a jihar.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum