WASHINGTON, D.C —
Yaduwar cutar coronavirus wadda ake alakantawa da wani wurin shakatawa na dare a birnin Seoul na kasar Koriya Ta Kudu, ya janyo tsana ga ‘yan luwadi.
Hakan na faruwa ne bayan da aka alakanta barkewar annobar da ‘yan luwadi masu zuwa wurin.
A yayin da Koriya Ta Kudu ta yi nasara wajen takaita yaduwar cutar corona cikin ‘yan makonnin nan, dada yaduwa da sabuwar bullar coronar ke yi, wadda ake alakantawa da wuraren shaye-shaye da shakatawa a birnin na Seol, ya janyo farbagar yiwuwar barkewar cutar a karo na biyu, da kuma kyamar ‘yan luwadi.
Daga cikin sabbin kamuwar, guda 29 ne aka tabbatar suna da nasaba da wani wurin shakatawar dare mai suna Itaewon, wanda ‘yan luwadi suka fi zuwa.
Facebook Forum