Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace lokaci yana kurewa gwamnatin shugaban kasar Syria Bashar al-Assad yayinda masu fafatukar kare damokaradiya suke kira ga Siriyawa su yi gangamin gama gari yau jumma’a na neman sauke shugaban kasar. Clinton ta bayyana haka ne yau jumma’a a wani taron kasashe masu rajin damokaradiya a Vilnius babban birnin kasar Lithuniya. Tace tilas ne gwamnatin tayi garambawul na zahiri ko kuma ta ci gaba da fuskantar tankiya. Clinton tace yunkurin Mr. Abbas na ba ‘yan hamayyar gudanar da taro sau daya rak cikin makon nan bai gamsar ba. Bisa ga cewarta, kyale ‘yan hamayyar su yi taro a Damascus yayinda kuma gwamnati ta tura tankokin yaki zuwa arewacin kasar bai nuna gwamnatin tana da kyakkyawar niya ba. Gwamnatin kasar Syria ta ci gaba da kai kazaman hare hare kan masu zanga zangar kin jinin gwamnati dake kira ga shugaban kasar ya sauka daga karagar mulki. A cikin tashin hankali na baya bayan nan, jami’an tsaro sun kashe a kalla mutane 12 a cikin kwanaki biyu yayin farmakin da sojoji suka kai kusa da kan iyakar kasar da Turkiya a arewa maso gabashin kasar.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace lokaci yana kurewa gwamnatin kasar Syria
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tace lokaci yana kurewa gwamnatin shugaban kasar Syria Bashar al-Assad yayinda masu fafatukar kare damokaradiya suke kira ga Siriyawa su yi gangamin gama gari yau jumma’a na neman sauke shugaban kasar.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024