Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yace ya ji dadin ganawar da yayi a liyafar cin abinci da Kim Yong Chol dan hannun daman shugaban Koriya ta arewa Kim Jong-un , gabanin tarurrukan da za su yi yau Alhamis 31 ga wata, akan yiwuwar yin taron koli cikin wata mai zuwa tsakanin Kim da Trump.
Pompeo ya sanya wani hoto a shafinsa na twitter, inda yake gaisawa da Kim Yong Chol, da kuma wani hoton da ya nuna manyan jami’an zaune a wani gida kusa da Shelkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York.
A yau din ne dai Pompeo ya fada a shafinsa na Twitter cewa, yiwuwar taron koli tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa zai ba Koriyar wata gagarumar damar cimma tsaro da habbakar tattalin arziki. Kim Yong Chol ne babban jami’in Koriya ta arewa da ya kawo ziyara Amurka cikin shekaru 18.
Sannan daga shi Pompeo na Amurka da kuma Chol ba wanda yayi magana da ‘yan jarida a lokacin da suka isa wurin liyafar cin abincin. Fadar shugaban Amurka ta kuma ce an shirya za su yi tarurruka da yawa a yau Alhamis din karshen watan nan na Mayun shekarar 2018 da muke ciki.
Facebook Forum