Kotun Koli na Amurka ta amincewa jihar Texas tayi amfani da dokar zabe da ta kafa a lokacin zabe d a za a yi cikin watan Nuwamba mai zuwa, duk da hukuncin da kotun kasa ta yanke cewa dokar zata hana tsiraru damar kada kuri’a.
Hukuncin kotun kolin da ta bayar a safiyar jiya Asabar ba’a sanya hanu akai ba, kuma bata bada dalilin daukar wannan mataki ba.
Dokar ta tilastawa masu kada kuri’a su nuna katin shaida da yake dauke da hotonsu kamin a bari su jefa kuri’a. Jami’an jihar Texas sun ce dokar an kafata ne domin hana magudin zabe, sun bayyana goyon bayansu da hukncin kotun kolin.
Amma alkali Ruth Bader Ginsburg ta bayyana rashin amincewarta da wannan hukunci wanda ya dauki shafi 6, tace hukuncin zai hana kusan ‘yan jihar dubu dari shida daga kada kuri’arsu. Amma jami’an jihar suka ce basu yarda da wannan adadi da alkali Ginsburg ta bayar ba.